Mark 6

Annabi Marar Daraja

1Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. 2Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majamiʼa, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka! 3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗanʼuwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ʼyanʼuwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

4Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ʼyanʼuwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” 5Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.

6Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu.

Yesu Ya Aiki Sha Biyun

Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.

8Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda-ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10Duk saʼad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku saʼad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”

12Suka fita, suna yi waʼazi, suna ce wa mutane su tuba. 13Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.

An Yanke Kan Yohanna Mai Baftisma

14Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a koʼina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”

15Waɗansu suka ce, “Ai, Eliya ne.”

Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”

16Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”

17Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka ɗaure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗanʼuwansa Filibus, wadda ya aura. 18Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗanʼuwanka.” 19Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba ta iya ba, 20domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk saʼad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yǎ ji shi.

21A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. 22Saʼad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.

Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.”
23Ya yi mata alkawari da rantsuwa, cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?”

Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”
25Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon: “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu yanzun nan.”

26Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yǎ hana ta ba.

27Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. 29Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.

Yesu Ya Ciyar da Dubu Biyar

30Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”

32Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. 33Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. 34Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.

35A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. 36Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”

37Sai ya amsa, ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.”

Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum
Girik zai ci dinari ɗari biyu
! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”

38Sai ya yi tambaya, ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.”

Da suka duba, sai suka ce, “Biyar-da kifi biyu.”

39Saʼan nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. 41Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. 42Kowa ya ci, ya ƙoshi, 43almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. 44Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.

Yesu Ya Yi Tafiya Kan Ruwa

45Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yǎ sallami taron. 46Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yǎ yi adduʼa.

47Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.

Nan da nan ya yi magana da su, ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
51Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52gama ba su fahimci alʼamarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.

53Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka ɗaure jirgin a ƙugiya. 54Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. 56Duk inda ya shiga-cikin ƙauyuka, birane ko karkara-sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yǎ bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.

Copyright information for HauSRK